Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiya ta dakile yunkurin kai mata hari da makamai masu linzami

Hukumomin Saudiya sun sanar da kakkabo makamai masu linzami 3 da aka harba yankin gabashin kasar mai arzikin man fetur, da kuma sassan biranen  Najran da Jazan a kudancin kasar.

Hoto domin misalin makami mai linzami.
Hoto domin misalin makami mai linzami. © Sebastian Apel/US Department of Defense/AP
Talla

Har yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai farmakin  na jiya Asabar, sai dai kawancen rundunar sojin da Saudiyya ke jagoranta wajen yaki da 'yan Houthi a Yemen, ya zargi yan tawayen da ake alakantawa da Iran.

Babu wanda dai ya rasa ransa a farmakin, sai dai wata majiya ta ce baraguzan makamin mai linzami da ya nufi gabashin Saudiya, wanda kuma aka tarwatsa shi a sararin samaniyar birnin Dammam, ya jikkata yara biyu na Saudiya, tare da lalata wasu sassan gidaje 14.

Hare-haren na zuwa ne kwanaki 4 bayan aika wani jirgi mara matuki da ya kai hari filin jirgin saman Abha da ke kudancin Saudiya, inda ya raunata mutane 8 tare da lalata wani jirgin farar hula.

'Yan tawayen Houthi na Yemen sun dade suna kai hare -hare kan Saudiya da ke jagorantar kawancen sojojin da suka shiga kasar Yemen a 2015, tare da goyon bayan dakarun hambararren Shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi da ke yaki da mayakan na Houthi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.