Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiyya ta yaye rukunin farko na sojoji mata

Ma'aikatar tsaron Saudiyya, ta yaye rukunin farko na sojoji mata daga cibiyar horas da dakarun kasar.

Wasu daga cikin kashin farko na sojoji mata da kasar Saudiyya ta yaye, bayan kammala karatun su daga cibiyar horas da mata ta rundunar soji.
Wasu daga cikin kashin farko na sojoji mata da kasar Saudiyya ta yaye, bayan kammala karatun su daga cibiyar horas da mata ta rundunar soji. © Al Arabiya
Talla

Karo na farko kenan a tarihin Saudiya da ake yaye dalibai sojoji mata da suka kammala daukar horon makwanni 14 da suka fara ranar 30 ga Mayu.

Tun cikin watan Fabarairu na wannan shekara Saudiya ta bai wa matan kasar damar neman shiga aikin na soji, inda ta takaita shekarun masu damar a tsakanin 21 zuwa 40.

A baya dai an san Saudiya da takaitawa mata shiga harkokin jama'a, amma a shekarar 2017, masarautar ta bai wa mata 'yancin tuka mota tare da ba su damar shiga filayen wasanni, sabon sauyin da aka fara gani a karkashin jagorancin Yarima mai jiran gado Muhammed bin Salman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.