Isa ga babban shafi
Saudiya

Saudiya ta fara daukar mata aikin soja

Ma’aikatar tsaron Saudi Arabia ta sanar da bude shafin fara daukar sabbin sojoji Mata tun daga ranar Lahadi, a wani yunkurin ba su damar yin gogayya da takwarorinsu Maza a fagen baiwa kasar tsaro.

Dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta a Yemen
Dakarun kawance da Saudiya ke jagoranta a Yemen AFP
Talla

Tun a safiyar Lahadi ne ma’aikatar tsaron Saudiya ta bude shafin daukar sojojin aiki ta Intanet, inda ta sanar da cewa kofa a bude ta ke ga matan da ke son shiga aikin na Soja wadanda shekarunsu na haihuwa ya kai 21 zuwa 40.

Sanarwar ta ce dukkanin wadanda za su cike bayanan neman aikin na Soja ba kadai ga Mata ba har da maza, dole sai sun cika sharuddan da aka gindaya na daukar aikin kama daga shekaru har zuwa tsayin Centimita 155 kan kuma dole sai ya zamana basa kowanne irin aiki na gwamnati.

Sauran sharuddan sun hada da cewa dole sai Matan na da shaidar dan kasa ta Saudiya kana ya zamana sun halarci makarantar gaba da sakandire haka zalika dole sai mace na na auren dan asalin kasar ta Saudiya.

Sanarwar ma’aikatar tsaron ta ce guraben aikin Sojin da Matan za su nema ya hada da Sojin kasa da na sama da na masarauta da na ruwa kana Sojin da ke kula da sashen manyan makamai na kasar sai kuma Sojojin da ke kula da sashen lafiya na Sojoji

Bugu da kari ma’aikatar ta sanar da cewa dole sai kowacce mace na da cikakkiyar lafiyar kwakwalwa da ta jikin iya aikin na Soji sai kuma an bi diddigin ba ta da tarihin cutar tabin hankali.

Wannan ne dai karon farko da Saudiya za ta dauki mata a matsayin Soji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.