Isa ga babban shafi
Iran - zanga-zanga

Malaman Iran sun gudanar da zanga-zanga a garuruwa sama da 100

Dubban malamai a kasar Iran suka gudanar da zanga-zanga a fiye da birane 100 domin nuna adawa da jinkirin kan albashinsu da kuma sauye-sauye kan fansho.

Jagoran juyin -juya halin kasar Ayatollah Ali Khamenei. 8/02/2022
Jagoran juyin -juya halin kasar Ayatollah Ali Khamenei. 8/02/2022 AFP - -
Talla

Zanga-zangar da aka yi a ranar Asabar ta kasance ta baya-bayan nan a jerin gangami da malamai da sauran ma’aikatan gwamnati ke gudanarwa a watannin baya-bayan nan sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da karancin samun kudaden shiga.

Jaridar Etemad mai rajin kawo sauyi ta ce malamai sun gudanar da zanga-zanga a wajen majalisar dokoki a Tehran babban birnin kasar da kuma gaban ofisoshin ma'aikatar ilimi a manyan lardunan da suka hada da Isfahan da Shiraz da kuma Mashhad.

Malaman sun shafe watanni suna bukatar gwamnati ta gaggauta aiwatar da sauye-sauyen da zai sa albashin su ya yi daidai da korewarsu da kuma kwazon su.

A makon da ya gabata ne majalisar dokokin Iran ta ce za a fara aiwatar da sabon tsarin da aka shafe sama da shekaru goma ana jira daga farkon sabuwar shekara ta Iran wadda za ta fara a ranar 21 ga watan Maris.

Masu zanga-zangar sun kuma bukaci a daidaita kudaden fanshonsu da na sauran ma’aikatan gwamnati.

Masu zanga-zangar sun kuma yi kira ga hukumomi da su saki malaman da aka tsare a zanga-zangar da aka yi a baya da a kara musu albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.