Isa ga babban shafi

Rasha ta yi asarar dakaru dubu 50 tun bayan faro yakinta a Ukraine - bincike

Wani bincike da manazarta yake-yake suka gudanar, ya gano cewa sojojin Rasha 50,000 ne suka mutu a rikicin da ke wanzuwa tsakanin ta da Ukraine, abin da ke nuna cewa an samu karuwar adadin wadanda suka mutu a wannan yakin a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Wasu sojin Rasha a fagen dagah.
Wasu sojin Rasha a fagen dagah. AFP - WOJTEK RADWANSKI
Talla

Kididdigar da kungiyar yada labarai mai zaman kanta ta Mediazona da gamayyar masana suka tattara ta ce adadin wadanda suka mutu ya kai 27,300 a tsawon shekaru biyun da Rasha ta dauka ta na yakar Ukraine, wanda hakan ke nufin ya karu da kashi 25 idan aka kwatanta da bara.

Amma adadin da Rasha ta fitar a hukumance a watan Satumban 2022 ya nuna cewa sojojinta kasa da dubu shida ne aka kashe.

Cibiyar Nazarin yake-yake ta duniya ta ce asarar da Rasha ta yi ya karu musamman a lokacin manyan hare-haren da aka kai a Donetsk, da kuma birnin Bakhmut.

Akalla biyu cikin biyar na mayakan Rasha da suka mutu ba su da wata alaka da aikin soji a hukumance, illa iyaka dai ana alakanta su da mayakan sa kai da ake daukowa daga cikin fararen hula, wasu kuma daga gidan yari.

Binciken ya lura cewa fursunoni dubu tara aka dauka ta hanyar kamfanin Wagner ko kuma kai tsaye daga ma’aikatar tsaron Rashan, kuma da dama daga cikinsu sun mutu ne a fagen daga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.