Faransa ta gargadi 'yan kasarta yin balaguro zuwa yankin Gabas ta tsakiya
Faransa ta gargadi ‘yan kasar ta game da tafiya zuwa kasashen Iran, Lebanon, Isra’ila da kuma yankunan Palasdinu a halin yanzu.
Wallafawa ranar:
Ministan harkokin wajen kasar Stephane Sejourne ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa a halin da ake ciki yana da matukar hadari yan kasar su ziyarci wadannan kasashe.
Wannan gargadi na zuwa ne bayan da Iran ta yi barazanar kai munanan hare-hare zuwa Isra’ila matsayin ramuwar gayyar da ta kai kan ofishin jakadancin ta dake Syria da yayi sanadin mutuwar mutune 7 ciki har jana-janar din soja guda biyu.
Wannan na nuna yadda rikici ke kara rincahbewa a gabas ta tsakiya, dalilin da ya sanya Faransar daukar aniyar fara kwashe jakadunta da ke Iran tare da Iyalan su, kuma ba za’a sake tura wani bafaranshe aiki a wadannan kasashe da aka lissafa ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu