Isa ga babban shafi

Kotun Vietnam ta yanke wa shahararriyar 'yan kasuwa hukuncin kisa kan rashawa

Wata Kotu a kasar Vietnam ta yankewa wata shahararriyar mai sana’ar gidaje da filaye Truong My Lan hukunci kisa, sakamakon samunta da hannu a badakalar kudade da yawan su ya kai dala biliyan 12 da miliyan 460, laifin almundahana mafi girma da aka samu a tarihin kasar.

Truong My Lan da kotu ta yankewa hukuncin kisa a Vietnam, bayan samunta da laifin cin hanci da rashawa.
Truong My Lan da kotu ta yankewa hukuncin kisa a Vietnam, bayan samunta da laifin cin hanci da rashawa. AP - Thanh Tung
Talla

A karshen zaman shari’ar na Alhamis din nan, an yankewa matar wadda itace shugabar kungiyar masu sana’ar sayar da gidaje da filaye ta kasar hukuncin kisa, bayan samunta da laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa da almubazzaranci da kuma take dokokin banki da tu’ammali da kudade.

An dai fara wannan shari’a ne a ranar 5 ga watan Maris din ta ya gabata, abinda ke nufin an kammala ta ba tare da wani bata lokaci ba.

Wannan hukunci ya zama wata ‘yar manuniya na cika alkawurran da jam’iyya mai mulki ta Communist Party ta dauka na yaki da cin hanci a kasar.

Wannan shi ne hukunci kan laifin almundahana mafi girma da aka taba gani a tarihin kasar, duk da dai an sha ganin yadda gwamnati ke tilastawa manyan jami’anta ko kuma ‘yan kasuwa sauka daga mukamansu idan an same su da wannan lafi.

Har yanzu lauyoyinta basu ce komai dangane da hukuncin ba, sai dai guda daga cikin iyalanta ya shaidawa manema labarai cewa uwar gida Lan za ta daukaka kara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.