Isa ga babban shafi

Ambaliya ta tilasta kwashe mutane dubu 110 daga Rasha da Kazakhstan

Koguna a kauyuka da biranen Rasha da Kazakhstan na ci gaba da tumbatsa sakamakon ambaliyar da ake fuskanta biyo bayan narkewar kankara wanda ya tilasta kwashe mutane fiye da dubu 110 dai dai lokacin da masana ke ci gaba da gargadin yiwuwar tsanantar lamarin kowanne lokaci a yanzu.

Kauyukan da dama ne ambaliyar ke kokarin shafewa a Rasha da Kazakhstan.
Kauyukan da dama ne ambaliyar ke kokarin shafewa a Rasha da Kazakhstan. AP - Anatoly Zhdanov
Talla

Yanayin yadda kankara da dusar kankara ke ci gaba da narkewa a Rashan ya tilastawa tumbatsar kogunan Rasha da kudancin Urals baya ga yammacin Siberia da kuma arewacin Kazakhstan wanda kuma ke barazana ga manyan biranen kasar.

Fiye da kwanaki 5 kenan koguna a biranen Moscow da Astana na ganin tumbatsar koguna da yanzu haka suka haddasa mummunar ambaliya lamarin da ya tilasta mahukuntan kasar sanya dokar ta baci.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce ambaliyar ta jefa Rasha a wani yanayi mai cike da tashin hankali kuma mafi muni da kasar ba ta gani ba cikin gomman shekaru da suka gabata.

A cewar kakakin na fadar gwamnatin Rasha ruwan na ci gaba da taruwa a yankunan da ba gurabensu ba, wanda kuma abin damuwa ne matuka.

Ko a jiya Laraba Kazakhstan ta sanar da kwashe mutane dubu 96 da 271 adadi mafi yawa da ta kwashe tun bayan farowar ambaliyar a makon jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.