Isa ga babban shafi

EU da Amurka za su karfafa alaka da Armeniya bayan ɓaɓewa da Rasha

Kungiyar tarayyar Turai ta yi alkawarin baiwa kasar Armenia tallafin yuro miliyan 270, dai-dai lokacin da turai da Amurka ke kokarin kara yaukaka alaka tsakanin su da kasar bayan da ta raba gari da Rahsa.

Shugabar kungiyar tarayyar Turai Ursula Vond der Leyen
Shugabar kungiyar tarayyar Turai Ursula Vond der Leyen REUTERS - ALINA SMUTKO
Talla

Wannan sanarwa na zuwa ne bayan tattaunawar da Prime ministan kasar Nikol Pashinyan da kuma shugabar kungiyar tarayyar Turai Ursula Von der Leyen da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken don karafafa alaka a tsakanin su.

Kasar dai na duba yiwuwar karfafa alakar tattalin arziki da kasashen yammacin duniya bayan ballewareta daga tsohuwar aminiyarta Rasha, bayan da kasar ta gaza dakatar da Azerbaijan daga yunkurin kutsawa cikinta.

Da take bayani Von Der Leyen ta ce tarayyar Turai zata fara bada wannan kudi ne a matsayin kashin farko don tallafawa Armeniya farfadowa daga magagain talauci datake fama a shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.