Bukatun Isra'ila na tsagaita wuta ba su yi dai-dai da na Falasdinawa ba - Hamas
Kungiyar Hamas ta ce bukatun da Isra'ila ta gabatar na tsagaita wuta a yakin da suke yi a Gaza, ba su yi dai-dai da bukatun bangaren Falasdinawa ba, amma za ta kara yin nazari kan tayin tare da mika matsayarta ga masu shiga tsakani.
Wallafawa ranar:
A karshen wata tattaunawa da wakilan bangarorin sukayi a birnin Cairo ne dai kasashen Masar da Qatar, da ke shiga tsakani suka mika wa Hamas bukatar Isra’ila kan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, bayan kwashe watanni 7 ana kai hare-hare yankin na Gaza.
Sai dai wasu al’ummar yankin Gaza sun ce Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama a tsakiya da kuma Kudancin Gaza a jiya Talata, ciki kuwa har da harin da ya hallaka iyalai 14 a Al-Nusseirirat.
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar da shirinsu na kai hari ta kasa a yankin Rafah, inda sama da fararen hula miliyan daya ke samun mafaka, duk kuwa da matsin lambar da kasashe suka yi masa na kaucewa hakan.
A wannan tattaunawa ta karshe da bangarorin suka yi a birnin Cairo na kasar Masar, ta samu halartar shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka William Burns, sai dai kuma an gaza cimma matsaya.
A karkashin yarjejeniya da za a cimma, Hamas na bukatar ganin Isra’ila ta daina kai hare-hare yankin Gaza tare da barin mutane su koma gidajensu da suka yi saura.
To sai dai a nata bangaren, Isra’ila na kokarin ganin ta kubutar da mutanenta da Hamas tayi garkuwa da su a ranar 7 ga watan Oktoban bara, tare kuma da kawo karshen mulkin da Hamas ke yi a yankin tun a shekarar 2007.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu