Isa ga babban shafi

Zaben kananan hukumomi a Turkiya ya koyawa shugaba Erdogan hankali

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin gyara duk wasu kura-kurai da suka kai ga kayar da jam'iyyarsa a zaben kananan hukumomi, inda 'yan adawa suka yi amfani da matsalar tattalin arziki wajen lashe zaben, lamarin da ya haifar da rashin tabbas kan shirinsa na yin garambawul ga kundi tsarin mulkin kasar.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan kenan, lokacin da ya isa rumfar zabe a birnin Istanbul, ranar 31 ga Maris, 2024.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan kenan, lokacin da ya isa rumfar zabe a birnin Istanbul, ranar 31 ga Maris, 2024. AP - Khalil Hamra
Talla

Kuri'ar da aka kada a ranar Lahadi ta nuna rashin nasara mafi muni da Erdogan da jam'iyyarsa ta AKP suka fuskanta a cikin sama da shekaru 20 da suka shafe suna mulkin kasar, lamarin da ya sake farfado da jam'iyyar adawa tare da karfafa matsayin magajin birnin Istanbul, Ekrem Imamoglu a matsayin babban abokin hamayyar shugaban.

Duk da cewa jam'iyyar AKP ta dade tana mamaye lungu da sako na kasar, sai dai a wannan jam'iyyar CHP ta lashe kuri'un jama'a a karon farko cikin shekaru da dama tare da mamaye mafi yawan manyan biranen kasar, inda ta ratsa yankunan da ke tsakiyar kasar Turkiyya masu ra'ayin rikau.

Manazarta sun ce masu kada kuri'a sun bayyana halin da suke ciki kan matsalar tsadar rayuwa, yayin da ake fama da hauhawar farashin kayayyaki da kusan kashi 70, abin da ake ganin ya haifar da rarrabuwar kan jama’a saboda salon siyasar Erdogan.

Sakamakon ya gurgunta fatansa na yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulki, wanda zai iya tsawaita mulkinsa har zuwa 2028 idan wa'adinsa ya kare, ko da yake bayanai sun nuna cewa, jam’iyyar AKP da kawayenta suna da rinjaye a majalisar dokokin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.