Isa ga babban shafi

Yau ake zagaye na biyu na zaben neman shugabancin kasar Turkiya

An bude rumfunan zabe a kasar Turkiya, a zabe zagaye na biyu na farko a kasar, inda shugaban mai ra'ayin mazan jiya Recep Tayyip Erdogan ke neman tsawaita wa’adin mulkinsa na tsawon shekaru 20 har zuwa shekarar 2028 idan ya samu nasara, da kuma abokin takararsa Kemal Kilicdaroglu.

Wasu allunan 'yan takarar zaben shugaban kasar Turkiya zagye na biyu tsakanin Recep Tayip Edogan and Kemal Kilicdaroglu.28/05/23
Wasu allunan 'yan takarar zaben shugaban kasar Turkiya zagye na biyu tsakanin Recep Tayip Edogan and Kemal Kilicdaroglu.28/05/23 AP - Khalil Hamra
Talla

Shugaba Erdogan ne ya samu mafi rinjayen kuri'u a zagayen farko na zaben da aka gudanar ranar 14 ga watan Mayu, amma ya gaza samun samun kaso da zai bashi lashe zaben kai tsaye a zagaye na farko.

Tun da kafe 8 na safe agogon kasar wato 5 a GMT aka bude rumfunan kada kuri'u, yayin da ake saran rufe su da karfe 5 na yamma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.