Isa ga babban shafi

An rantsar da Erdogan a karo na biyar a matsayin shugaban Turkiya

An sake rantsar da shugaban Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban kasar Turkiya a karo na uku, bayan da ya lashe zaben zagaye na biyu karo na farko da aka taba gudanarwa a kasar.

Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan.
Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan. AP - Ali Unal
Talla

Shugaban mai shekaru 69 da ya kwashe sama da sheakaru 20 ya na mulkin kasar, a yanzu zai sake jagorantar ta na tsawon shekaru 5, kuma nan gaba kadan ake saran ya sanar da ‘yan majalisar zartarwar sa wadanda za su tunkari kalubalen tattalin arzikin da kasar ke fuskanta.

A lokacin bikin rantsarwar da ya gudana a zauren majalisar dokokin kasar wanda kuma ya samu halartar shugabannin kasashen daban-daban, Erdogan ya sha alwarin gudanar da gwamnati ba tare da nuna wariya ko san kai ba.

Wannan ne karo na biyar da Erdogan ke jagorantar kasar, domin kafin zawoma shugaban kasa, ya taba yin faraminista karo biyu tsawon shekaru 10, sannan ya zamo shugaban kasa na tsawon shekaru 10, yanzu kuma ya dora a kan hakan.

Shugaban ya samu nasarar lashe zaben zagaye na biyu da aka gudanar a ranar 28 ga watan daya gabata duk kuwa da hadakar da jam’iyun adawar kasar suka yi, ga matsalar tattalin arziki da kuma ta ibtila'in girgizar kasar da aka samu a watan Fabuwairu da ya yi sanadiyar mutuwar mutane samada dubu 50.

Erdogan ya samu kashi 52.18 na kuri’un da aka kada, ya yin da babban abokin hamayyar sa Kemal Kilicdaroglu ya samu kashi 47.82.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.