Isa ga babban shafi

MSF tace yawan 'yan gudun hijira a yankin arewa maso yamman Najeriya ya kai kusan dubu 600

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa MSF ta koka game da karancin kayayyakin agaji ga wadanda ke cikin tsananin bukata a arewacin Najeriya, lura da yadda aka samu karuwar mutanen dake tserewa muhallin su.

Tambatrin kungiyar MSF
Tambatrin kungiyar MSF © Julie Remy/msf.fr
Talla

Ta cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce karancin kayan na zuwa ne dai-dai lokacin da tashin hankali da ayyukan ta’addanci ke kara dai-daita mutane musamman a arewa maso yammacin kasar.

Baya ga karancin kayan tallafin, kungiyar ta kuma koka kan karuwar cututtuka, rashin abinci mai gina jiki, yayinda kungiyoyin bada agaji suka yi biris da yankin.

Matsalar tashin hankali, taɓarɓarewar tattalin arziƙi da sauyin yanayi sunsa aƙalla mutane 600,000 suka rasa matsuguni a arewa maso yammacin Najeriya a ƴan shekarun baya-bayan nan a cewar kungiyar.

A bara dai an samun alamun kwarin gwiwar samun tallafi daga guraren da suka dace, amma kungiyar na ganin cewa kudaden da suka yi saura yanzu haka ba zasu ishi al’ummar da ke neman agajin ba.

Wannan matsala bata tsaya iya arewa maso yammacin kasar ba, ta tsallaka har zuwa ga arewa maso gabas, a sakamakon yadda mayakan Boko Haram suka dawo da ayyukan su da karfi bayan sauki da aka samu na ‘yan lokuta.

A jawabin sa, jagoran kungiyar likitocin bada agaji na ƙasa da ƙasa MSF Ahmed Bilal yace kungiyar ta jima tana mika koken ta gaban majalisar dinkin duniya da kungiyoyin bada agaji kan yadda jama’a ke kara fadawa cikin tashin hankali, amma da alama koken nasu ba ya kaiwa ga nasara.

Mazauna jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina sune matsalolin tashin hankali na hare-haren ƴan bindiga, garkuwa da mutane sukafi shafa a arewa maso yammacin Najeriya.

A bara kaɗai sama da mutane 2,000 aka kashe a hare-hare sama da 1,000 a yankin, cewar hukumar dake tattara bayanan rikici wato Armed conflict Location & Event Data Project.

Haka zalika mutane da dama sun rasa sana'o'in su musamman yadda tashin hankali yah ana su komawa gidajensu ko gonakinsu.

Asusun tallafawa kananan yar ana majalisar dinkin duniya UNICEF ya kiyasta cewa akalla akwai kananan yara miluyan 2.6 dake fama da matsananciyar cutar yinwa a ƙasar, inda ya ce  yara 532,163 na rayuwa a jihohin Sokoto, Katsina da Zamfara.

Wasu 'yan Jihar Zamfara da hare-haren 'yan bindiga ya tilasta musu gudun hijira a wani gini dake karamar hukumar Anka.
Wasu 'yan Jihar Zamfara da hare-haren 'yan bindiga ya tilasta musu gudun hijira a wani gini dake karamar hukumar Anka. © Benedicte Kurzen/NOOR

Karuwar cututtukan da ke addabar yara          

Ana samun ƙaruwar ɓarkewar cututtukan da za'a iya kare kamuwa da su, kamar Zazzaɓin cizon sauro, amai da gudawa, sanƙarau, ƙyanda da mashaƙo, inji kungiyar ta MSF.

A shekarar 2023, jami'an MSF a arewa maso yammacin Najeriya sun magance matsalar cutar zazzaɓin cizon sauro da ya kai 169,954, sai kuma cutar amai da gudawa 4,462, sai cutar sanƙarau 1,548, ƙyanda 1,850, sannan sai mashaƙo 13,290.

Game da raguwar kudaden talafin Wakilin ƙungiyar MSF a Najeriya Dr. Simba Tirima yace akwai takaici yadda wannan matsala ta shafi ko ina a duniya, inda ya ce kasancewar kungiyar ta dogara ne kachokan kan tsarin bada tallafi na majalisar dinkin duniya ya kara ta’azzara lamarin.

Kungiyar na takaicin yadda ayyukan tallafi musamman na bayar da abinci suka ragu
Kungiyar na takaicin yadda ayyukan tallafi musamman na bayar da abinci suka ragu REUTERS

Bukatar Kungiyar MSF 

Kungiyar ta ce akwai bukatar masu ruwa da tsaki a fannin bayar da agaji da hadin gwiwar gwamnatin Najeriya su gaggauta kai dauki musamman ga mutanen da ke cikin halin ni ‘yasu.

MSF ta ce ya zama dole a samo hanyoyin samar da kudaden shiga cikin sauri don ceto mutane da ke galabaita saboda yunwa, yayin da kananan yara ke mutuwa a sakamakon kamuwa da cututtukan da ke da alaka kai tsaye da yunwa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.