Isa ga babban shafi

Yadda azumin bana ya riski al'ummar Musulmi a sassan duniya

Al’ummar musulmi a fadin duniya sun tashi da Azumin watan Ramadan na bana yau Litinin, ba tare da samun rarrabuwar kawuna game da ganin wata kamar yadda aka saba gani a baya ba.

Mafi yawan kasashen duniya sun tashi da azumin a yau Litinin
Mafi yawan kasashen duniya sun tashi da azumin a yau Litinin REUTERS/ Ammar Awad
Talla

Ba kamar yadda aka saba  a baya ba, a bana an ga watan na Ramadan akan lokaci a kusan dukannin kasashen duniya, lamarin da ke tabbatar da yau Litinin matsayin daya ga watan na Ramadan.

Azumin na bana ya riski al’ummar musulmi kusan biliyan 2 a fadin duniya a yanayi daban-daban da ya shafi matsin tattalin arziki, tsadar rayuwa da kuma yake-yake.

Yadda Azumin ya riski ‘yan Africa

A kasashe irin su Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi da ke yammacin Africa jama’a sun fara azumin cikin karuwar rashin tsaro, matsanancin talauci, sauyin yanayi da kuma tsadar rayuwa da ke walagigi da mutanen su.

Kasashen da ke cikin na kan gaba masu yawan al’ummar musulmi a nahiyar Africa na fatan gwamnatoci zasu yi ruwa da tsaki wajen kawo karshen wadannan matsaloli.

A yankin gabashin Africa ma kusan haka abin yake, inda azumin ya riski kasashe irin su Kenya, Uganda da Rwanda cikin mastin tattalin arziki da tsadar rayuwa, su kuwa al’ummar jamhuriyar dimokradiyyar Congo sun marabci azumin cikin fargabar yaki da tashin hankali da kuma hare-haren M23 da sauran kungiyoyin masu rike da makamai.

Duk da kiraye-kirayen kasashen duniya, amma har yanzu babu wata tartibiyar yarjejeniyar tsagaita wuta a tsakanin bangarorin da ke rikici a Sudan mai yawan al’ummar musulmi, lamari da ba shakka zai kara tsananta azumin ga jama’ar su.

Masar, Habasha da Somalia suma dai duk babu wani sauyi game da rikive-rikice tsakanin ‘yan tawaye da dakarun gwamnati da kuma tsananin talauci da ke addabar ‘yan kasar.

Azumin 2024
Azumin 2024 © AFP / JEWEL SAMAD

 

Yadda Azumin ya riski gabas ta tsakiya

Duk da yadda wannan yanki na duniya yayi kaurin suna wajen rashin zaman lafiya, amma jama’a sun jima basu fara azumi ciki fargaba da rashin tabbas irin na bana ba, wannan kuwa ya faru ne saboda ruwan wutar da Isra’ila da shafe wattani biyar tana yi a Gaza, da kuma martani ta hanyar kai hari da mayakan Houthi na Lebanon ke kaiwa jiragen ruwan kasashe da ke yunkurin shigar da kaya Isra’ila ta kan tekun Maliya, yayin da wannan yaki ke barzanar fantsama zuwa sauran kasashe makwafta.

Ko a tattaunawar da aka zauna juma’ar da ta gabata tsakanin Hamas da Isra’ila an tashi ne baram-baram ba tare da cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta saboda  Ramadan din ba.

Isra’ila ta sha alwashin ci gaba da barín wuta, ba tare da la’akari da masu azumin ba, har sai Hamas ta bi dukannin ka’idojin da ta gidaya mata, dokokin da Hamas ta yi fatali da su.

Kasashe a wannan yanki na ci gaba da zaman doya da manja, ganin yadda aka ki fitowa kiri-kiri a nuna goyon baya ko akasin haka ko kuma kira ga Isra’ila da tsagaita wuta.

 

Azumi na cikin manyan ibadun da ke da muhimmanci a addinin musulunci
Azumi na cikin manyan ibadun da ke da muhimmanci a addinin musulunci REUTERS/Faisal Al Nasser

 

 

 

Yaya aka fara azumi a Turai

Turawan yammacin duniya ma ba’a bar su a baya ba wajen fara azumin na bana ba duk kuwa da fargabar rashin ingantaccen tsaro a kasashe irin su Faransa da Amurka, yayin da ake fama da matsin tattalin arziki a Burtaniya da makwaftanta sai kuma tsadar rayuwa da Belgium da Jamus da sauran su.

Azumin bana a yankin Asia

Yankin Asia da ya kunshi kasashe irin su China, Japan, Koriya da sauran su a iya cewa azumin na bana ya riski jama’a da sauki-saukin rayuwa, idan an kwatanta da sauran sassan duniya, duk da rikicin kan iyaka da ke tashi lokaci-lokaci tsakanin China da Taiwan, sai kuma gwaje-gwajen muggan makamai da Koriya ta arewa ke yi sa’i da lokaci.

Akwai dama-dama a fannin tsadar abinci da kuma karfin tattalin arziki, yayin da ake da zaman lafiya mai inganci idan aka kwatanta da sauran sassan duniya.

Bisa al’ada dai al’ummar musulmi kan kwashe tsahon kwanaki 29 ko kuma 30 suna azumtar watan na Ramadan da ke da matukar muhimanci a gare  su, yayin da yake cikin manyan ginshikan da ke rike da adddinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.