Isa ga babban shafi

Sojan Amurka ya cinna wa kansa wuta don nuna adawa da yakin Gaza

Wani jami'in sojin Amurka da ya banka wa kansa wuta domin nuna adawa da yakin da Isra'ila ke yi a Gaza ya mutu kamar yadda Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon ta sanar a hukumance a yau Litinin.

Aaron Bushnell, jami'in sojin saman Amurka da ya kashe kansa a harabar ofishin jakadancin Isra'ila a birnin Washington.
Aaron Bushnell, jami'in sojin saman Amurka da ya kashe kansa a harabar ofishin jakadancin Isra'ila a birnin Washington. © Réseaux sociaux
Talla

A jiya Lahadi ne jami'in sojin saman na Amurka sanye da kaki ya cinna wa kansa wuta a harabar ofishin jakadancin Isra'ila da ke birnin Washington da misalin karfe 6 na yamma agogon GMT, wato karfe 1 na rana kenan agogon Washington.

Rahotanni na cewa, mutumin ya dauki kansa a hoton bidiyo, yana fadin " A bai wa Falasdinu 'yanci" a daidai lokacin da yake kona kansa da wuta, inda ya samu munanan raunukan da suka yi sanadiyar ajalinsa.

A cikin bidiyon wanda ya karade kafafen sada zumunta, an jiyo sojan na cewa, " ba zai yi tarayya ba wajen aikata kisan kiyashi".

Duk da cewa, hukumomin da ke kula da ofishin jakadancin sun yi kokarin ceto ransa ta hanyar kashe wutar da ke ci a jikinsa tare da ruga wa da shi asibiti, amma abin ya ci tura.

Mai magana da yawun Ofishin Jakadancin Isra'ila ya ce, babu wani ma'aikacinsu da ya samu ko kwarzane a yayin faruwar wannan al'amari kuma ba su ma san mutumin ba a cewarsa.

Wannan na zuwa ne a yayin da zanga-zanga ke ci gaba da karade wasu sassan Amurka domin nuna adawa da ayyukan Isra'ila a Zirin Gaza.

Yakin ya samo asali ne sakamakon harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 1,400.

Kimanin Falasdinawa dubu 30 ne suka rasa rayukansu tun bayan da Isra'ila ta fara kaddamar da harin ramuwar gayya a Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.