Isa ga babban shafi

Kungiyar Afrika ta AU ta goyi bayan Falasdinawa a yakinsu da Isra'ila

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Falasdinu a rikicin da ake ci gaba da fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da kungiyar ta bukaci kasashe mambobinta da su katse hulda da Isra'ila.

Shugabannin kasashen AU
Shugabannin kasashen AU AFP - MICHELE SPATARI
Talla

Wata sanarwa da AU ta fitar ta ce, kungiyar na goya wa Falasdinawa baya a fafutukarsu ta nuna adawa da mamayar Isra'ila tare da hankoron maido da 'yancinsu gami da samun kasarsu mai cin gashin kanta.

A makon jiya ne a yayin gudanar da taronta, kungiyar AU mai mambobi 54 ta yi tur da abin da Isra'ila ke aikatawa a Gaza, tana mai kira ga 'ya'yanta da su kawo karshen huldar kasuwanci, kimiya da musayar al'adu da Isra'ila.

Kazalika AU ta yi kira ga kasashen duniya da su yi la'akari da ka'idojin nan na jin kai ga bil'adama da kuma adalci.

AU ta kuma bayyana fushinta kan abin da ta bayyana a matsayin cin mutuncin bil'adama da ake yi a Zirin Gaza wanda ya samo asali daga sojojin Isra'ila.

Har ila yau, kungiyar ta Afrika ta bayyana fargabarta game da yiwuwar fadadar yakin Gaza zuwa wasu kasashe makota kamar Lebanon da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.