Isa ga babban shafi

Kotu ta yankewa Dani Alves hukuncin shekaru 4 a gidan yari

Wata kotu a kasar Spaniya ta yankewa tsohon dan wasan Bercelona kuma dan asalin kasar Brazil Dani Alves hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yari sakamakon kama shi da laifin aikata fyade.

Tsohon dan wasa Dani Alves yayin da yake karbar hukunci
Tsohon dan wasa Dani Alves yayin da yake karbar hukunci via REUTERS - POOL
Talla

Tsohon dan wasan mai shekaru 40 a duniya na cikin ‘yan wasan masu kwalisa a tarihin kwallon kafa, sai dai ya musanta zargin da ake yi masa na yiwa matar fyade a safiyar ranar 31 ga watan Disamban 2022.

Sai dai kuma lauyansa ya bukaci kotu ta bashi damar daukaka kara kasancewar har yanzu yana kan bakan sa cewa matar sharri ta yi masa.

An dai zargi Alves da yaudarar matar zuwa cikin bandaki a wani gidan rawa abinda Alves din ya musanta, sai dai ya ce ko a lokacin ya bata damar tafiya idan bata sha’awar aikata masha’ar amma ta amince don haka babu fyade a cikin lamarin.

A sanarwar bayan yanke hukunci da kotun ta fitar ta ce hujjoji sun nuna cewa Alves din ya aukawa matar ne ba tare da son ranta ba.

Bayan hukuncin shekaru 4 da kotu ta yanke masa, ta kuma ci shi tarar yuro dubu 150.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.