Isa ga babban shafi
ZABEN PAKISTAN

Harin mayakan IS ya kashe karin mutum tara a Balochistan

Akalla mutum tara ne ciki har da kananan yara biyu suka mutu, yayin wani hari da aka kai a Pakistan yau Alhamis, daidai lokacin da al’ummar kasar ke kada kuri’a a babban zaben kasar.

Lokacin da jami'an tsaro ke bincike a yankin Qillah Saifullah da ke yankin Baluchistan na kasar Paksitan, bayan wani mummunan hari da 'yan ta'addan suka kaddamar.
Lokacin da jami'an tsaro ke bincike a yankin Qillah Saifullah da ke yankin Baluchistan na kasar Paksitan, bayan wani mummunan hari da 'yan ta'addan suka kaddamar. © Zain Ullah / AP
Talla

An dakatar da sabis din wayoyi da kuma rufe iyakokin kasar ta Pakistan, duk domin shiryawa wannan zabe mai cike da zarge-zargen tafka magudi da kuma tashin hankali.

A jiya Laraba ne aka samu mutuwar gomman mutane, suma saboda harin bam din da aka kai kudu maso yammacin kasar.

Daga bisani kungiyar masu tayar da kayar baya ta IS ta dauki alhakin kai wadannan hare-hare.

An jibge dubban jami’an tsaro a kan hanyoyi da rumfunan zabe a sassan kasar da kuma kan iyakokin da suka raba Pakistan din da Iran da kuma Afghanistan.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun ruwaito cewa ‘yan sanda hudu aka kashe, yayin wani wari da ‘yan ta’adda suka kai musu daidai lokacin da suke aikin sintiri a yankin Kulachi.

Haka zalika an kai hari da gurneti a sassan Balochistan, sai dai kuma jami’an tsaro na ci gaba da sanya idanu a rumfunan zabe, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar.

An gano dogon layi na masu kada kuri’a a rumfunan zabe gabanin fara dangwale, duk da fargabar da ake ciki na sha’anin tsaro da kuma tsananin sanyi da ake fama da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.