Isa ga babban shafi

Yawan wadanda suka mutu a gobarar dajin Chile ya kai mutane 131

Adadin wadanda suka mutu sakamakon gobarar dajin da ta tashi a wani yanki da ke gabar tekun Chile ya karu zuwa mutane 131.

Yadda gobarar dajin da ta shafe kwanaki 5 tana ci ta tafka barna a wasu yankunan kasar Chile.
Yadda gobarar dajin da ta shafe kwanaki 5 tana ci ta tafka barna a wasu yankunan kasar Chile. © Javier TORRES / AFP
Talla

Kwararrun masu bincike kan kwayoyin hallitar dan Adam a kasar ta Chile dai sun dukufa wajen aikin tantance ragowar gawarwakin wadanda suka kone a gobarar dajin da ta tashi a karshen makon da ya gabata.

Kimanin mutane dubu 20, suka rasa muhallansu a dalilin iftila’in, bayan da karfin iska da kuma yanayi na tsananin zafi suka kara rura wutar dajin da ta tafka mummunar barna, gobarar da masana suka bayyana a matsayin ta uku mafi muni da aka gani a cikin wannan karni.

Tuni dai gwamnatin Chile ta kaddamar da bincike kan zargin ko wasu miyagu ne suka kunna wutar dajin da gangan, wadda ya zuwa yanzu aka gaza tantance yawan daruruwan mutanen da suka bace a dalilinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.