Isa ga babban shafi

Faransa ta bukaci daukar mataki a kan naman da ake samarwa a dakunan kimiya

Duniya – Kasar Faransa ta bukaci kungiyar EU da tayi bayani karara a kan abinda ake nufi da naman da ake samarwa a dakunan binciken kimiya sabanin wadanda ake samarwa ta hanyar kiwon dabbobi domin kare lafiyar 'yan kasar ta.

Firaministan faransa Gabriel Attal
Firaministan faransa Gabriel Attal AFP - JULIEN DE ROSA
Talla

Firaministan kasar Gabriel Attal ya gabatar da wannan bukatar a yunkurin kwantar da hankalin manoman kasar wadanda suka kwashe makwanni suna zanga zanga a kan irin matsalolin dake shafar noma da kiwon da suke yi.

Attal yace a tsarin irin abincin da mutanen kasar Faransa ke amfani da shi, babu abinda ake kira 'synthetic meat' ko kuma naman da aka samarwa a dakin binciken kimiya, saboda haka ne suke bukatar kungiyar EU tayi doka karara dangane da halarcin sa.

Yadda manoman Faransa suka girke taraktocin su a kan tituna domin nuna fushin su ga gwamnati
Yadda manoman Faransa suka girke taraktocin su a kan tituna domin nuna fushin su ga gwamnati © Reuters - Abdul Saboor

A watan jiya, ministocin kula da ayyukan noma na kasashen Faransa da Austria da kuma Italia sun kaddamar da wani hadin kai inda suka bukaci masana su yi mahawara a kan irin wannan naman, wanda suke cewa bai dace a sayar da shi a kasashen dake nahiyar Turai ba, saboda hukumar dake kula da inganci abinci a yankin bata bada damar cin sa ba.

Kasashen Austria da Italia sun bukaci gudanar da binciken masana da kuma gudanar da gwaji a kan irin wannan naman domin tabbatar da rashin illar sa ga jama'a.

Yadda manoman Turai yau suka yi arangama da jami'an tsaro wajen taron shugabannin EU
Yadda manoman Turai yau suka yi arangama da jami'an tsaro wajen taron shugabannin EU AFP - DIRK WAEM

Masu kare muhalli na kallon irin wannan naman a matsayin wanda zai taimaka wajen kare muhalli daga illar da dabbobi ke haifarwa, yayin da masu kare hakkin dabbobi suka ce wannan naman zata rage mutuwar dabbobi da kuma yanka wadanda basu da koshin lafiya domin amfanin jama'a.

Kasar Italia a watan Nuwambar bara ta kafa dokar haramta amfani da irin wannan naman ko kuma sayar da shi a cikin kasar ta, yayin da hukumomin Amurka da Singapore suka bada damar amfani da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.