'Yan ci rani kusan 100 sun yi batan dabo a tekun Meditareniya cikin 2024
Hukumar kula da ‘yancirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa Kusan bakin haure 100 ne suka mutu ko kuma suka bace a tsakiya da gabashin tekun meditereniya tun farkon shekarar 2024, wanda ya ninka adadin da aka samu a bara a irin wannan lokacin.
Wallafawa ranar:
Hukumar ta IOM tayi wannan bayani ne a wani babban taro dake gudana a birnin Rom na kasar Italiya, wanda ya samu halartar gomman shugannin Afirka da na Turai domin tattauna batutuwan ci gaban tattalin arziki da kuma hanyoyin magance matsalar bakin haure dake tafiya Turai.
Bayanan binciken ayyukan da aka gudanar game da mutuwa ko bacewar bakin haure a baya bayannan an samu mutane dubu 3 da 41 da ko sun bace ne ko kuma sun mutu tekun meditereniya, a shekarar da ta gabata a kokarinsu na shiga turai.
A farko farkon wannan wata ne wasu ‘yancirani 40 ‘yan kasar Tunisia suka yi batan dabo a wani babban kwale kwale daya nufi gabar tekun Italiya.
Tunisia dai ta maye gurbin Libya a matsayin wata muhimmiyar kafa da bakin haure ke bi domin ficewa kasashen saboda tserewa taluaci ko kuma yake-yake.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu