Isa ga babban shafi

Manoman Faransa sun ci gaba da zanga zangar adawa da harajin gwamnati

FARANSA – Manoma a kasar Faransa yau sun ci gaba da gudanar da zanga zangar su a fafutukar ganin an rage musu harajin a kan amfanin gonarsu da kuma sauya sabbin manufofin dake yiwa sana’arsu illa.

Manoman Faransa a cikin taraktocin su a birnin Paris  REUTERS/Stephane Mahe
Manoman Faransa a cikin taraktocin su a birnin Paris REUTERS/Stephane Mahe REUTERS - STEPHANE MAHE
Talla

Manoman sun ce zanga zangar ta su wadda ta shiga mako ta biyu zata ci gaba da gudana har sai an biya musu bukatunsu, matakin dake zama babban kalubale ga sabon Firaministan kasar Gabriel Attal.

Shugaban kungiyar matasa manoma ta kasar, Arnaud Gaillot ya shaidawa manema labarai cewar, kome na iya faruwa da fafutukar ta su, musamman ganin yadda ta haifar da matsala zirga zirgar ababan hawa.

Wasu kafofin yada labaran Faransa sun ruwaito hukumomin leken asirin kasar na gargadin gwamnati a kan yadda kungiyoyin manoman suka yi kira ga mambobinsu da su hallara a birnin Paris domin ci gaba da zanga zangar.

Farmers gather during a highway blockade, Tuesday, Jan. 23, 2024 near Beauvais, northern France.
Yadda manoman suka tare wata babar hanya kusa da Beauvais dake arewacin France. AP - Matthieu Mirville

Yanzu haka manoma da dama sun tuka motocin nomansu na tarakta zuwa birnin domin shiga zanga zangar tare da jibge kayan noman a kan tituna.

Firaministan kasar ya gayyaci manyan ministoci domin tattauna yadda za’a tinkari matsalar tare da shirin gabatar musu da sabon matsayin gwamnati gobe juma’a, ganin shugaba Emmanuel Macron na ziyarar kasar India.

Wani manomi mai shekaru 61, Jean-Jacques Pesquerel yace a ko da yaushe gwamnati dora musu sabbin haraji take yi, yayin da ribar noman da suke samu ke raguwa.

Masu zanga zangar sun zubar da kwandunan timatirin da kabejin da aka shiga da shi kasar daga kasashen ketare a biranen Marseille da Lyon, birane na biyu da na 3 mafi girma a kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.