Isa ga babban shafi

Wani jirgin fasinja ya yi hatsari a Afghanistan akan hanyarsa ta zuwa Rasha

afghanistan – Hukumar da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen sama ta Rasha, Rosaviatsia ta bayyana cewa wani karamin jirgin fasinja da ke kan hanyarsa ta zuwa Moscow daga Indiya ya yi batan-dabo.

Tasiwirar dake nuna kasashen Afghansitan, Pakistan da Iran
Tasiwirar dake nuna kasashen Afghansitan, Pakistan da Iran © Studio graphique FMM
Talla

Ana zaton jirgin ya fadi ne a wani tsauni da ke arewa maso gabashin Afghanistan.

Jirgin saman ya yi hatsari ne a lardin Badakhsan wanda ke da iyaka da China da Tajikistan da kuma Pakistan a ranar lahadin nan, sai dai babu tabbaci kan daidai wurin da jirgin ya fadi.

Zabihullah Amiri, wanda jami'in watsa labarai da al'adu ne na lardin ya bayyana cewa tuni aka aika da jami'ai wurin da hatsarin ya faru a yankin Topkhana wanda ke a gundumar Kuran-wa-Munjan.

"Jirgin saman ya yi hatsari amma ba a san takamaimai wurin da ya fadi ba. Mun tura jami'ai sai dai ba su dawo ba," kamar yadda Amiri ya bayyana ba tare da wani karin bayani ba.

"Jama'ar gari ne suka gaya mana hakan da safe," in ji shi.

Tsaunin Hindu Kush ya bi ta lardin wanda a nan tsauni mafi tsawo a Afghanistan yake, wato tsaunin Noshaq inda yake da tsawon mita 7,492.

Hukumar da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen sama ta Rasha Rosaviatsia ta bayyana cewa wani karamin jirgin fasinja da ke hanyar zuwa Moscow daga Indiya ya batan-dabo a Afghanistan.

Hukumar ta ce jirgin kirar Falcon 10 jet, yana da rajista a Rasha kuma akai mutum shida a cikinsa, daga ciki akwai ma'aikatan jirgin hudu da fasinja biyu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.