Isa ga babban shafi
China

China na bincike kan jirgin da ya yi hadari da mutane 132

Wani jirgin fasinja na kamfanin Chine Eastern dauke da fasinjoji 132 ya yi hadari a litinin din nan, wanda hukumar kulada zirga-zirgar sufirin jiragen saman kasar tace, jirgin kirar Boeing 737 ya taso ne daga birin Kunming inda ya nufi kudancin Guangzhou.

Jirgin saman China Airlines
Jirgin saman China Airlines AFP/File
Talla

Hukumomin sun ce akwai fasinjoji 123 sai kuma ma’aikatan jirgin 9 a cikin sa.

Faruwar lamarin dai ta ja hankalin al’umma ciki harda shugaba Xi Jinping wanda ya bayyana kaduwar sa da kuma bada umarnin gudanar da bincike nan ta ke.

Hukumomin kamfani sifirin sun tabbatar da faruwar lamarin, sai dai basu bada alkaluman adadin wadanda suka mutu ko kuma suka kubuta daga hadarin ba.

Tuni dai kamfanin ya mika sakon ta’aziyar sa ga iyalan fasinjojin da kuma ma’aikatan sa da hadarin ya rutsa da su.

Rabon da a samu mummunar hadarin jirgin sama a China tun a shekarar 2010 wanda ya yi sanadiyar mutumar mutane 42 daga cikin fasinjoji 92 da ke cikin jirgin.

A tarin China, mummumar hadarin jirgin da ya afku a kasar shine na kamfani Northwest a shekarar 1994 wanda dukkanin fasinjoji 160 da ke ciki suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.