Isa ga babban shafi

Shugabanr Brazil ya ce, babu batun yafewa mutanen da suka yi kokarin murkeshe Demokradiya a kasar.

Shugaban kasar Brazil Lula, ya rufe kofar tuba ga wadanda suka jagoranci zanga zangar lalata fadarsa ta Brazilia a shekarar da ta gabata. Shugaba Lula ya  bayyana   cewa,  babu batun afuwa ga wadanda  su ka aikata laifin kokarin murkushe demokradiya.

Президент Бразилії Лула де Сілва
Shugaban Brazil Anacio Lula Dasilva © Annegret Hilse / Reuters
Talla

Furucin na zuwa ne kuma a dai dai wanan lokaci da aka cika shekara guda da barkewar zanga zangar da  mamaye fadar shugabancin kasar ta Brazila a shekarar da ta gabat jim kadan bayan bayyana samun nasarar lashe zaben shugabancinb kasar da Inacio Lula Dasilva ya yi , inda dubban magoya bayan tsohon shugaban kasar mai tsatsauran ra''ayi Jay Bolsonaro suka mamaye fadar shugabancin kasar tare da lalata wani sashen fadar.

A lokacin da Ya ke gabatar da jawabi a taron  majalisar dokokin kasar, shugaban na Barazil ya bayyana cewa, dukkanin wadanda suka dau nauyi da kudade, da wadanda suka shirya kuma suka zartar da yinkurin juyin mulkin,  za su fuskanci hukumci na musaman, kuma babu afuwa ga wanda ya yi yinkurin haifar da tarnaki ga mulkin demokradiya da kuma cutar da al'ummar kasarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.