Isa ga babban shafi

Amurka ta ce tabbas kungiyar mayakan IS ne suka kai wa Iran hari.

Hukumar tara bayanan sirri ta Amurka, ta ce tabbas, reshen kungiyar IS a kasar Afghanistan ne ya kai hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 100 cikin makon jiya a kasar Iran.

Iranian President Ebrahim Raisi attends a meeting with Russian President Vladimir Putin in Moscow, Russia December 7, 2023
shugaban Iran Ibrahim Ra'isi via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Majiyoyi wadanda suka bukaci a sakaye sunanyensu, sun tabbatar da kafafen yada labaran Amurka cewa, ko shakka babu IS a Afghanistan ce ta tsara tare da kai wadannan hare-hare, a daidai lokacin da ake tunawa da cika shekaru 4 da mutwar janar Qassem Sulaimani, wani babban kwamandan sojin Iran da Amurka ta kashe a Iraqi.

Kasar Iran dai ta Zargi Amuruka da Isra’ila da kai harin tare da daukar al’kawalin mayar da martani mai karfi a kan duk wanda ta tabbatar da hannunsa a harin da ya yi sanadiyar muruwar mutane kusan 100 wasu kuma da dama suka jikkata. Kawo yanzu dai duk da ikrarin na Amurka, kawo yanzu dai kungiyar ta IS, ba ta fito ta bayyana alhakin daukar nauyin harin da ae cike da shakku a kansa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.