Isa ga babban shafi

Sarauniyar Denmark ta yi murabus daga kujerarta

Sarauniyar Denmark Margreth ta biyu, ta sanar da ajiye mukaminta tare da mika shi ga danta Yarima mai jiran gado Fredrik.

Sauniyar Denmark Margrethe II ta sauka daga kujerarta.
Sauniyar Denmark Margrethe II ta sauka daga kujerarta. AP - Ida Marie Odgaard
Talla

Saruniyar wadda ta fi kowacce dadewa kan karaga a nahiyar Turai, ta sanar da hakan ne a wata tattaunawar kai tsaye da aka yi da ita a kafar talabijin din kasar.

Mai shekaru 83, Sarauniya Margreth ta dare kan sarautar kasar ne tun shekarar 1972, kuma cikin jawabin ta na sabuwar shekara, tayi bankwana da jama’ar kasar kusan miliyan 6.

Sarauniyar ta ce tuni aka fara shirye-shiryen mika mulkin ga wanda zai gajeta a ranar 14 ga wannan watan Janairu, kuma ta roki jama’ar kasar da su baiwa dan ta hadin kan da suka bata don tabbatar da ci gaba kasar da kuma alkinta al’adu.

Saruniyar ta ce lokaci yayi da ya kamata ta huta sakamakon tsufa da ya cimmata da kuma rashin lafiya da take fama da ita.

Bayanai sun ce Sarauniyar na fama da matsanacin ciwon baya, inda har aka yi mata tiyata a watannin baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.