An binne gawar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta II
Masarautar Ingila ta fitar da sanarwar cewa an binne gawar Sarauniya Elizabeth ta II, bayan kammala bikin bankwana da ita a ranar Litinin.
Wallafawa ranar:
Talla
An binne ta tare da marigayi mijinta, Duke na Edinburgh, a inda aka binne mahaifinta, da mahaifiyarta da kuma 'yar'uwarta.
Da tsakar ranar Litinin, aka saukar da akwatin gawar Sarauniya Elizabeth a cocin St George's Chapel, da ke cikin fadar Windsor.
Wannan ya zo ne a karshen bikin bankwana, kuma da shi ne aka kawo karshen taron jana'izar marigayiyar sarauniyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu