Isa ga babban shafi
SHARHIN JARIDUN DUNIYA

Yawan damfara na neman hana 'Yan Najeriya hada-hadar kudade ta internet

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a Tarayyar Najeriya ta yi sharhi game da yadda alummar kasar suka fara hakura da yin amfani da tsarin hada-hadar kudi ta internet saboda yawan damfara da zarar wa mutane kudade a asusunsu babu gaira babu dalili da bankunan kasar ke yi.

Jaridu dauke da labarai daga sassan duniya
Jaridu dauke da labarai daga sassan duniya AFP/File
Talla

A cewar Darektan hukumar sadarwa da hulda da jama’a na Kasar Bashir Alhassa, a shekarar nan kawai hukumar ta samu kararaki sama da 248 na matsalar damfara daga kwasatamomi masu asusun ajiya a bankunan kasar, kamar yadda jaridar ta ruwaito.

Shalkwatar babban bankin Najeriya CBN a birnin Abuja.
Shalkwatar babban bankin Najeriya CBN a birnin Abuja. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE

Premium times ta kuma ruwaito Kwamitin dake yaki da ayyukan damfara ta internet, ya ce a cikin watan Yunin shekarar nan kawai an yi hasarar kudi da yawansu ya kai naira biliyan 9 da miliyan 500 daga masu damfara ta shafukan internet.

'Yan bindigan jihar Filato sun sake barazanar kai wasu sabbin hare-hare

Jaridar Punch ta ruwaito ‘Yan bindigan da suka kai hare-hare a ungwanni 17 da ke kananan hukumomin Bukos da Barikin Ladi, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 195, sun sake yin barazanar kai wasu sabbin hare-hare cikin sakon wasikar da su ka aika wa mazauna ungwar Pushit dake karamar hukumar Mangu a jihar Filato.

Wata Unguwa da rikici ya daidaita a jihar Filaton Najeriya
Wata Unguwa da rikici ya daidaita a jihar Filaton Najeriya AFP - -

Punch ta ce jami’in hulda da jama’a na jihar Alabo Alfred ya ce Rundunar ‘Yan Sandan ta samu labarin sakon wasika na barazana da ‘yan bindigan suka aika, kuma ta na a cikin shirin ko ta kwana domin dakile duk abinda ka iya biyo baya.

Punch ta kuma ruwaito mazauna kauyen pushit sun shaida mata cewa suna rayuwa ne a cikin dar-dar tun bayan samun sakon barazanar sake kai musu wani sabon hari.

'Yan bindigan Zamfara sun ba iyayen daliban da suka sace wa'adin kwanaki 7 

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Iyayen daliban jami’ar Gusau dake jihar Zamfara, wadanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su sun yi kira Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta taimaka wajen ceto ‘ya’yansu cikin lokaci.

Iyayen daliban dai sun bukaci gwamnati ta tattauna da ‘yan bindigan kamar yadda ta saba a lokacin da hare haren Kungiyar Boko Haram ya kai kololuwa a yankin arewa naso gabashin kasar.

Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau
Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Gusau Fugus facebook

Tun a ranar alhamis dai ne iyayen daliban suka mika koken su, sakamakon barazanar da ‘yan bindigan suka yi na fara kashe wasu daga cikin daliban mata, muddin ba a biya musu bukatunsu ba.

An gudanar da jana'izar bai daya na mutanen da gobara ta kashe a Laberiya

Jaridar Observer da ake wallafawa a Laberiya ta ruwaito labarin gudanar da jana’izar bai daya na mutane 40 da rayukansu ya salwanta a gobarar da ta tashi bayan fashewar wata tankar dakon gas a yankin Totota dake arewacin kasar.

Jaridar ta ce Kungiyar Agaji ta Red Cross dake kasar da hadin gwiwar Ma’aikatar Lafiyar kasar ne suka shirya jana’izar mamatan da iftila’in ya rutsa da su, wadanda daga cikin su akwai wata mata mai juna biyu, da ‘yar ta da kuma mijinta. Haka ma bayaga mamatan ana cigaba da kai wa wadanda suka jikkata doki.

Jana'izar bai daya na wasu matattu
Jana'izar bai daya na wasu matattu REUTERS/Edgar Su

Observer ta kuma ce a daren talatar da ta gabata dai ne, tankar dakon gas din ta yi hadari a yankin na Totota da ke lardin Bong kuma nan take ta fashe, wanda ya yi sanadiyar hallaka tarin mutanen da ke kusa da ita. Haka ma jaridar ta ce an dora alhakin yawan haduran da ake samu a Liberia da lalacewar hanyoyi, dalilin da ya mayar da kasar dake yammacin Afrika a matsayin wadda ta fi fuskantar hadarin mota tsakanin takwarorinta.

Gwmnatin Ivory Coast zata fara fitar da iskar gas zuwa Guinea

Jaridar Fraternite Matin da ake wallafawa a Ivory Coast ta ruwaito cewa kasar zata fara fitar da lita miliyan 50 na iskar gas kowanne wata zuwa kasar guinea, sabanin lita miliyan 70 da ta bukata, biyo bayan fashewa da gobabar da ta auku a babbar ma’adanan man fetur na kasar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 24 tare da jikkata wasu 454.

Fraternite Matin ta ce Côte d'Ivoire da ta sanar da batun sabon tsarin fitar da yawan iskar gas din zuwa Guinea ba ta bayyana tsawon lokacin da za ta shafe ta na gudanar da aikin ba

Ma'adanar Man Guinea da ta yi gobara a ranar 18 ga watan disamban 2023
Ma'adanar Man Guinea da ta yi gobara a ranar 18 ga watan disamban 2023 © Reuters / Souleymane Camara

Jaridar ta kuma ruwaito tun a ranar laraba da ta gabata ne Ministan tattalin arzikin Guinea Moussa Cissé, ya gana da Ministan Mai da albarkatun kasar Ivory Coast, Mamadou Sangafowa Coulibaly a birnin Abidjan game da yarjejeniyar da suka kulla na Shirin aika da iskar gas din.

Guguwar Tornado ta yi mumunar ta'adi cikin wasu yankuna a Birtaniya

Jaridar Mirror da ake wallafawa a Birtaniya ta ruwaito cewa sama da gidaje 100 ne suka lalace sakamakon kakkarfar guguwar Tornado da ta afkawa mazauna garin Stalybridge da sanyin safiyar jiya laraba.

jaridar ta ce guguwar da ta yi gudu da karfin maki tsakanin 137 zuwa 160, ita ce irin ta ta farko cikin shekaru 17 da Birtaniya ta taba gani.

Wani Yanki da guguwar Tornado ta lalata
Wani Yanki da guguwar Tornado ta lalata REUTERS/Rick Wilking

Mirror da ta wallafa wasu daga cikin ta’adin da guguwar ta haifar, ta kuma ruwaito cewa hotunan bidiyo sun nuna yadda guguwar ta yi ta kwashe rumfunan gidaje, da yadda kayayaki iri iri su ka yi ta yawo a iska, bayaga motoci da sauran dukiyoyin alumma da suka lalace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.