Isa ga babban shafi
Sharhin Jaridun duniya

Matsalolin da Najeriya za ta tsunduma a ciki a shekarar 2024

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Babban Bankin Duniya ya yi hasashen cewa nan da watan Mayun shekarar 2024 matsalolin tsaro da hare-haren ‘yan bindiga za su ci gaba da addabar wasu sassan jahohin Najeriya irin Borno da Katsina da Sokoto da Yobe da Zamfara da kuma jihar Adamawa.

Wasu jaridu na Najeriya
Wasu jaridu na Najeriya AP - Ben Curtis
Talla

A cewar jaridar Babban Bankin Duniyar ya yi wannan hasashe ne la’akari da yadda matsalar matsin tattalin arziki ke hana a samu bunkasa a bangaren noma na Kasar.

Punch ta kuma ce ana sa ran yawan hatsin da za a samu daga yankin yammaci da tsakiyar Afrika cikin shekarar 2023 dinnan da shekarar 2024 ya kai ton miliyan 76.5, adadin da ya ragu da kashi 2 bisa wanda aka samu a kakar da ta gabata. Kuma duk da haka ana sa ran kasashen Chadi da Mali da Nijar da kuma Najeriya su fi kawo kaso mafi yawa na yawan hatsin da ake sa ran samu.

Sama da mutane dubu 10 sun tsere daga gidajensu a Myanmar

Jaridar eleven da ake wallafawa a Myanmar ta ruwaito mazauna lardin Kawkareik dubu 10 sun tsere daga matsugunansu, inda suka nemi mafaka a ungwanni 3 da ke lardin Hpa-na sakamakon yakin da ake gwabzawa a wurin, kuma a cewar cibiyar dake kula da ‘yan gudun hijirar wannan yankin mutanen na tsanannin bukatar abinci da magunguna

Yanzu haka dai sansanonin ‘yan gudun hijira 3 da suka hada da garin Nab una dauke da ‘yan gudun hijira dubu 4,489 yayin da a Paikyone mutane dubu 2,679 ke da akwai, sannan garin Donrin ‘yan gudun hijira 3,520 ke rayuwa a wurin, abinda ken una duka duka a lardin Hpa-an adadin yan gudun hijirar da suka nema mafaka a wurin ya kai 10,688.

Ma'auratan da suka kashe kada mafi girma a duniya

Jaridar citizen da ake wallafawa a Tanzania ta ruwaito  wasu ma’aurata ‘yan asalin kasar murka da suka shahara wajen farautar namun daji sun haifar da hazo bayan sun kashe kada mafi girma a duniya da ke kasar Tanzania.

Josh da Sarah Baowmar dai sun wallafa hotuna da bidiyon kadar rataye a kan itace a shafinsu na instagram, inda suke ikirarin kafa tarihin kashe kada mafi girma a duniya.

A dayan bangaren kuwa kamar yadda jaridar citizen ta ruwaito wani jami’I daga hukumar dake kula da gandun daji a kasar Tanzania da ya bukaci a sakaya sunansa, wanda ya ce sun samu labarin faruwar lamarin, ya bayyana takaicinsa da yadda wasu ‘yan kasar ke taimakawa wajen yada bidiyon, lamarin dake cigaba da harzuka alumar kasar. Sannan a karshe yace nan ba da jimawa ba za su fitar da sanarwa a hukumance

Bakin-hauren Gambia sun koma gida daga Tunisia

Gwamnatin Gambia da hadin gwiwar Hukumar Kula da Bakin-haure ta Majalisar Dinkin Duniya sun mayar da gomman ‘yan Gambia da adadinsu ya kai 141, wadanda suka makale a Tunisia gida.

Jaridar Foroya ta ce tun bayan da hukumar ta soma gudanar da aiki a Gambia cikin shekarar 2001, wannan ne kaso mafi yawa na ‘yan gudun hijirar da aka mayar gida lokaci guda, bayan da suka kama hanya zuwa Turai domin nemawa kansu rayuwa mai kyau.

Cutar amai da gudawa ta yi kamari a Sudan

Hukumar Bayar da Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin Sudan da ya ki ci ya ki cinyewa na ci gaba da haifar da tsaiko wajen tunkarar bullar cutar amai da gudawa, wadda ke ci gaba da yaduwa a sassan kasar.

Hukumar ta ce adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar a cikin wata guda ya karu zuwa kusan mutane dubu 8,300, daga ciki akwai sama da dubu 1 da 800 daga jihar Al Jazirah. Jihar da a cikin watan nan ke fama da kazamin rikice rikice tsakanin rundunar sojin sudan da dakarun RSF, wanda yayi sandaiyar daidaita akalla mutane dubu 300.

Sanarwar hadin gwiwa da ma’aikatar lafiyar Sudan da Hukumar lafiya ta duniya suka fitar na cewa ya zuwa ranar 23 ga watan disamban nan da muke ciki, sama da mutane 200 daga jahohi 9 ne cutar ta kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.