Isa ga babban shafi

Kisan da aka yi wa yara a Gaza shi ne irinsa na farko a tarihi

Adadin kananan yaran da aka kashe a Yammacin Kogin Jordan da kuma Gabashin Birnin Kudus a bana, ya kai wani mataki da ba a taba ganin irinsa ba kamar yadda Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana.

Wasu kananan yara a Zirin Gaza
Wasu kananan yara a Zirin Gaza REUTERS - IBRAHEEM ABU MUSTAFA
Talla

Darektar UNICEF a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika, Adele Khodr ta bayyana cewa, an kashe kananan yara 83 a cikin makwanni 12 da suka gabata, adadin da ya rubanya wanda aka samu a shekarar 2022.

Sama da kananan yara 576 ne aka raunata, sannan aka tsare wasu da dama kamar yadda darektar ta bayyana a cikin wata sanarwa.

Babbar Jami’ar ta UNICF ta  koka kan yadda kasashen duniya suka zura ido suna kallon mummunan abin da ke faruwa a Zirin Gaza, inda yaran da ke Yammacin Kogin Jordan ke gamuwa da bala’i, ganin yadda suke cikin tsoro da bakin ciki a kodayaushe.

Rahotanni na cewa, fargaba ta dabaibaye rayuwar yau da kullum ta yaran, inda har wasu daga cikinsu ke tsoron zuwa makaranta ko kuma gudanar da wasa a waje saboda barazanar harbe-harben bindiga.

Yanzu haka hukumar ta UNICEF ta bayyana damuwarta game da hakkokin kananan yaran da ake takewa a Yammacin Kogin Jordan da kuma Gabashin Birnin Kudus, tana mai kira da a samar musu da tsaro da kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.