Isa ga babban shafi

Yan majalisar dokokin kasar Danmark, sun amince da wata doka da ta haramta kona al'kur'ani a bainar jama'a

Majalisar dokokin kasar Danmark ta amince da wata doka da ta haramta kona kur’ani a bainar jama’a, biyo bayan zanga zangogin da aka sha yi a kasashen musulmi, kan yadda ake ci gaba da kone Kur’ani a bainar jama’a, al’amarin da ke neman jazawa kasar matsalolin tsaro masu karfi.

wasu mata na karatun al Kuráni a Dacca,  6 novembre 2020.
wasu mata na karatun al Kuráni a Dacca, 6 novembre 2020. Munir UZ ZAMAN / AFP
Talla

Ayar dokar, da ta gabatar da wannan haramci, na karkashin tsarin  rashin mutunta addinan  wasu al’ummomi ne, aka kada kuriar amincewa da ita a jiya alhamis, inda ta  samu amincewar yan majalisun dokoki  94 kan 77 da ke adawa, a majalisar dokokin Folketing, mai kunshe da kujeru 179 na yan majalisa.

Idan dai ba a manta ba yawaitar kone konen alkur’anai da makiya musulunci a kasar ke yi ya haifar da tada jijiyoyin wuyan musulmi a kasashe da dama na duniya, tare da kira ga mahukumtan kasar da su dau matakan da za su kawo karshen wannan mummunar dabi’a da   za ta iya jefa kasar cikin matsaloli da dama, da suka hada da tattalin arziki da tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.