Isa ga babban shafi

Ba zan zama shugaban kama karya ba, idan kuka sake zabe na - Trump

Duniya – Tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya shaidawa magoya bayansa cewar muddin suka sake zabensa a shekara mai zuwa, ba zai zama shugaban kama karya ba.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump AP - Sue Ogrocki
Talla

Yayin da yake amsa tambayoyi lokacin halartar wani taron ganawa da magoya bayansa dangane da irin shugabancin da zai yi, da kuma ko zai dauki matakan ramuwa a kan abokan adawarsa, Trump yace sam ba zai yi haka ba, sai dai a lokaci guda.

Trump yace rana gudan da yake magana a kai, itace amfani da damar da yake da ita wajen rufe iyakar kasar da Mexico da kuma fadada aikin hakar man fetur a kasar.

Shugaba Trump dake neman wa'adi na biyu a zaben da ake hasashen cewar zasu fafata da shugaba Joe Biden na jam'iyyar democrat, ya sha fadin cewar zai dauki fansa a kan abokan adawarsa idan ya samu mulki.

Daga cikin wadanda yake tunanin daukar fansa a kansu, harda shugaba Joe Biden da masu gabatar da karar da suka tuhume shi da aikata tarin laifuffuka da ma'aikatan shari'a da kuma wasu jami'an gwamnati.

Trump wanda ke sahun gaba cikin mutanen dake neman jam'iyyar Republican ta tsayar takarar zaben shekara mai zuwa, na fuskantar tuhume tuhume da dama a kotu da ake ganin watakila su hana shi tsayawa takarar zaben mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.