Isa ga babban shafi

Yau za a gurfanar da Trump a gaban kotu

A wannan Alhamis ake sa ran gurfananr da tsohon shugaban Amurka Donald Trump a gaban kotu  kan tuhume-tuhumen da ake yi masa na yunkurin sauya sakamakon zaben 2020.

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump
Tsohon shugaban Amurka Donald Trump © AFP - PATRICK T. FALLON
Talla

Watakila wannan shari’ar ta haifar da cikas ga burin tsohon shugaban na Amurka na sake komawa fadar White House a zaben 2024 a daidai lokacin da ake ganin cewa, shi ne jam’iyyar Republican za ta tsayar domin yi mata takara.

An dai kafa shingaye na karfe a kewayen harabar kotun tarayyar ta E. Barret Prettyman da ke birnin Washington, inda za a tsare tsohon shugaban na Amurka wanda aka zarga da tunzura magoya bayansa har suka kaddamar da farmaki a ginin majalisun Amurka na Capitol a ranar 6 ga watan Janairun 2021.

Tun da safiyar yau aka  girke jami’an ‘yan sanda a harabar kotun, yayin da ‘yan jarida daga kafafen yada labarai daban-daban  na duniya suka yi dafifi tun cikin daren da ya gabata domin daukar rahotanni.

Ana sa RAN Trump mai shekaru 77 zai ki amsa aikata laifin da ake zargin sa da shi  a wannan shari’ar da za a fara gudanar da ita da misalin karfe 8 agogon GMT.

A karo na uku kenan tun daga watan Maris da ake tuhumar Trump da aikata miyagun laifuka, amma tuhumar ta yau ta fi wadanda aka yi masa a baya daukar hankali saboda girmanta, domin kuwa za ta iya hana shi komawa kan kujerar shugabancin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.