Isa ga babban shafi
RIKICIN ISRA'ILA DA FALASDINU

Tarihin musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Falasdinu

Sama da Falasdinawa 14,000 aka kashe a Gaza, tun bayan harin ranar 7 ga watan Oktoba, yayin da a Isra'ila, mutum 1,200 ne aka tabbatar harin Hamas ya kashe.

Un garçon tient un papier disant « Palestine libre » lors d'une manifestation contre Israël et en soutien aux Palestiniens à Sarajevo, en Bosnie, le dimanche 22 octobre 2023.
Yadda aka gudanar da zanga-zangar goyon Falasdinu a Bosnia kenan. AP - Armin Durgut
Talla

Isra’ila dai ta fuskanci matsi wajen sako Falassdinawan da ta tsare a gidajen yari, domin sako Yahudawan da ke hannun Hamas.

Ga biyar daga cikin cikin musayar fusrnunonin da ya wakana tsakanin Isra’ila da Hamas.

A ranar 23 ga watan Nuwambar 1983 ne Isra’ila ta sako Falasdinawa 4,500 domin musayar gawawwakin sojojinta shida da aka kama.

Kana a watan Mayun 1985 kuma, aka yi musayar Falasdinawa 1,150 domin karbar gawar sojojin Isra’ila uku bayan tsawon watanni ana tattaunawa akai.

An kuma yi musayar wanda ya samar da Hamas, wato Ahmed Yassin, a ranar daya ga watan Oktoban 1997, tare da wasu gomman Falasdinawa da na Jordan domin sako wasu Yahudawa biyu.

Isra’ila ta sako fursunoni 430, ckinsu kuwa har da ‘yan kasar Lebanon 23 a ranar 29 ga watan Janairun 2004, yayin wata musaya da kungiyar Hezbollah, domin karbar wasu sojojinta uku da aka yi garkuwa da su aka kuma kashe.

Bayan shekaru biyar, wani soja mai suna Gilad Shalit, da Hamas ta cafke shi a iyakar Gaza a watan Yunin 2006 lokacin yana da shekaru 19, ya samu iskar ‘yanci a ranar 18 ga watan Oktoban 2011.

An dai yi musayar wannan soja da wasu Falasdinawa 1,027, kuma a wancan lokacin, karon farko kenan da aka samu sojan Isra’ila a raye tun bayan shekaru 26 da Hamas ta dauka tana kame su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.