Isa ga babban shafi

Dole ne a bai wa asibitin Al-Shifa da ke Gaza kariya - Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce dole ne a kiyaye tsaron asibitin Al-Shifa yayin da ake gwabza fada a kusa da ginin asibitin da ke birnin Gaza, kuma kalaman nasa sun zo ne yayin da Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya bukaci Isra'ila da ta yi dukkan mai yiwuwa wajen kare fararen hula, inda ya bukaci a bayar da damar aiwatar da ayyukan jin kai cikin gaggawa. 

Harabar asibitin Al Shifa da ke Zirin Gaza.
Harabar asibitin Al Shifa da ke Zirin Gaza. © AFP - KHADER AL ZANOUN
Talla

Isra'ila ta zargi Hamas da boye mayakanta a cibiyar lafiyar ta Al-Shifa wadda hukumomin asibitin suka musanta hakan. 

Asibitin mafi girma a Gaza, Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana shi a matsayin tamkar makabarta, wanda ta ce ciki da wajensa gawawwaki ne suka mamaye. 

Da yawa daga cikin jarirai da lokacin haihuwarsu bai cika ba, da kuma masu fama da ciwon koda 45 da ke bukatar wankinta kusan ko yausshe, ba za su samu kulawar da suke bukata ba, saboda karancin lantarki. 

Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana ci gaba da gudanar da aikin jigilar kwalaben renon bakwaini daga wani asibiti a Isra'ila zuwa Gaza. 

Isra'ila ta fara kai hare-hare a Gaza bayan hare-haren Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba, inda aka kashe mutane 1,200 tare da yin garkuwa da fiye da 200. 

Ma'aikatar Lafiya ta Hamas ta ce an kashe Falasdinawa fiye da 11,000 a Gaza kuma daga cikinsu fiye da 4,500 kananan yara ne. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.