Isa ga babban shafi

Asibitoci sun zama makabartu a Gaza

Yayin da dakarun Isra’ila suka ja daga a harabar asibitoci da ke birnin Gaza, bayanai sun ce ala dole aka fara haka manyan kaburbura a cikin asibitoci domin binne mutanen da suka rasa rayukansu. 

Asibitin Al-Shifa da ke Gaza.
Asibitin Al-Shifa da ke Gaza. © KHADER AL ZANOUN / AFP
Talla

Dr. Mostapha Khaalout, Daraktan Asibitin Rentissi da ke kusa da babban asibitin Gaza ta Al-Shifa, ya bayyana halin da ake ciki sakamakon yadda jami’an tsaron Isra’ila suka hana jama’a kwashe gawarwakin ‘yan uwansu, inda ya ke cewa,

Komai ya tsaya cak a asibitinmu, duk da cewa akwai dubban kananan yara da ke jinya a cikinsa. Daga ciki akwai masu fama da cutukan zuciya yayin da wasu ke fama da curutuka kamar na kansa da kuma na koda.   

Dr, Khaalout ya kara da cewa, "A asibitin Shiffa kuwa, lamarin ya yi muni matuka. Tuni sojojin Isra’ila suka mamaye asibitin a daidai lokacin da adadin wadanda ke mutuwa ke dada karuwa. Jami’an kiwon lafiya ba za su iya yi musu jana’iza ba saboda da zarar suka yi yunkurin fita daga cikin ginin, nan take za a bude musu wuta."   

Yanzu haka hukumomin kiwon lafiya a Gaza sun shiga tashin hankali kan yadda karnuka suka fara kewayawa asibitocin Gaza sakamakon warin gawarwakin da suke shaka, inda ake fargabar za su iya kacalcala naman gawarwaki da zarar sun yi arangama da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.