Isa ga babban shafi

An harbe wani dan jarida mai shekaru 57 a kasar Philippines

A yau Lahadi aka harbe wani dan jaridan gidan rediyo a gidansa da ke kasar Philippines, kamar yadda ‘yan sanda suka sanar, a kasar da a kullum ake kai wa kafafen yada labarai hari kisan gilla da kuma tursasawa.

makiruho
makiruho © Pixabay/Michal Jarmoluk
Talla

Dan jaridar mai suna Juan Jumalon, mai shekaru 57, yana gidansa a tsibirin Mindanao da ke kudancin kasar, lokacin da wani dan bindiga ya harbe shi, a cewar Deore Ragonio, shugaban 'yan sanda na Calamba a lardin Misamis dake arewa maso yammacin tsibirin.

Mutumen da ake  zargin ya shiga dakin watsa shirye-shirye sa na rediyo, inda ya ce yana son yin sanarwa ta iska, kamar yadda wata sanarwa da ‘yan sanda suka fitar.

makiruho
makiruho © Pixabay

Bayan aikata wannan kisa, ya gudu, sai dai dan jaridar  Jumalon ya rasu a wani asibiti da ke yankin.

shugaban 'yan sanda Ragonio ya shaidawa AFP cewa " Juan Jumalon yafi magana ne akan al'amuran yau da kullum kuma ba a san shi da sukar kowa ba a cikin shirye-shiryensa."

Aikin jarida a yankin Asiya
Aikin jarida a yankin Asiya © Studio graphique FMM

Kungiyar 'yan jarida ta kasar Philippines (UNJP) ta yi Allah wadai da wannan "mummunan kisa."

Kasar Philippines na daga cikin kasashen da suka fi fuskantar matsalar ‘yan jarida, inda ba kasafai ake gurfanar da masu aikata irin wannan cin zarafin ba.

A watan Mayu, an harbe dan jaridar gidan rediyo Cresenciano Bunduquin a kofar gidansa da ke tsakiyar tsibirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.