Isa ga babban shafi

Mayakan Hezbollah sun yi artabu da sojojin Isra'ila

Sojojin Isra’ila da mayakan Kungiyar Hezbollah na Lebanon sun yi artabu ta kan iyakar kasashen biyu a yau Asabar, inda kowanne bangare ke ikirarin samun nasara a farmakin da ya kaddamar.

Yadda sararin samaniya ya turnuke da hayaki bayan Isra'ila ta kaddamar da hari kan Hezbolla ta kan iyakar kasarta.
Yadda sararin samaniya ya turnuke da hayaki bayan Isra'ila ta kaddamar da hari kan Hezbolla ta kan iyakar kasarta. AP - Hussein Malla
Talla

Wannan dai na zuwa ne kwana guda da shugaban Kungiyar Hezbollah, Hassan Nasrallah ya yi gargadin cewa, yakin da ake gwabzawa tsakanin  Isra’ila da mayakan Hamas a Zirin Gaza, ka iya rikidewa zuwa wani gagarumin rikici a yankin gabas ta tsakiya muddin Isra’ilar ta ci gaba da kai wa Falasdinawa hari.

Isra’ila ta ce ta mayar da martani saboda makamin atilari da aka cillo mata daga Lebanon, amma babu wanda ya rasa ranta daga cikin jama’arta a cewarta.

Falasdinawa dubu 400 sun makale a arewacin Gaza

Manzan musamman na Amurka David Satterfield ya bayyana cewa, akwai kimanin mutane dubu 350 zuwa dubu 400 da yanzu haka ke zaune a yankin arewacin Gaza, a daidai lokacin da sojojin Isra’ila suka yi wa birnin  kawanya.

Isra’ila ta shaida wa jama’ar Gaza da su fice daga yankin arewacin birnin zuwa kudanci a daidai lokacin da sojojinta suka zafafa hare-haren kan Hamas.

A bangare guda, kasar Turkiya ta sanar da janye dakadanta daga Isra’ila saboda yadda Isra’ilar ta ki amincewa da tsagaita musayar wuta a Zirin Gaza.

An yi zanga-zangar kin jinin Amurka da Isra'ila a Iran

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zanga a sasan Iran don nuna adawarsu ga Amurka da Isra’ila tare da nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da ke can Zirin Gaza da yaki ya daidaita.

Masu zanga-zangar da suka yi dandazo a harabar ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tehran sun yi ta rera wake-waken Allah-wadai ga Amurkar da kuma aminiyarta Isra’ila.

Kazalika sun kona wani mutun-mutumi na Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kuma tutar Amurka.

Tun lokacin da Hamas ta kai harin ranar 7 ga waotan Oktoban da ya gabata, tankiya ta tsananta tsakanin Iran da Amurka.

Zelensky ya koka kan yadda aka daina maganar Ukraine

 

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya koka kan yadda hankulan kasashen duniya suka karkata kan yakin Zirin Gaza, inda suka mance da  yakin da kasarsa ke gwabzawa da Rasha.

Zelensky ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai tare da Shugabar Hukumar Gudanarwar Kungiyar Kasashen Turai, Ursula von de Leyen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.