Isa ga babban shafi

Girgizar kasa a Nepal ta kashe mutane 132

Akalla mutane 132 ne suka mutu sannan wasu fiye da 100 suka jikkata sakamakon wata girgizar kasa da ta afku a wani yanki mai nisa na yammacin kasar Nepal, kamar yadda jami'an yankin suka sanar da safiyar yau Asabar.

Wani gida da ya rushe yan lokuta bayan girgizar kasa
Wani gida da ya rushe yan lokuta bayan girgizar kasa © Prime minister office / via Reuters
Talla

An auna girgizar kasa mai karfin awo 5.6 a zurfin kilomita 18 bisa ga binciken  kasa na Amurka .

 Iftila’in ya afkawa kasar Himalayan mai nisa a yammacin ranar Juma'a. Wurin ya kasance mai nisan kilomita 42 kudu da gundumar Jumla, ba da nisa da kan iyaka da Tibet ba.

Kakakin 'yan sanda na lardin Karnali Gopal Chandra Bhattarai, ya shaida wa AFP cewa, adadin wadanda suka mutu ya kai 132, yayin da wasu 100 suka jikkata.

Dakarun kasar Nepal na kai dauki yankunan da aka fuskanci girgizar kasa
Dakarun kasar Nepal na kai dauki yankunan da aka fuskanci girgizar kasa via REUTERS - NEPAL ARMY

Ya kara da cewa "keɓancewar gundumomin yana da wahalar isar da bayanai."

Hotunan bidiyo da hotuna da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda mazauna garin ke tono baraguzan gine-gine a cikin duhu domin fitar da wadanda suka tsira daga gine-ginen da suka ruguje. Yana nuna gidajen laka da aka lalata da wadanda suka tsira a waje don kare kansu daga wata rugujewar.Girgizar kasa ta zama ruwan dare a Nepal.

Wani yankin Nepal
Wani yankin Nepal AFP/File

Girgizarwar ta biyo bayan sa'o'i da dama bayan girgizar kasa mai karfin awo 4 a wannan yanki, a cewar hukumar ta USGS. An ji motsi girgizar kasa har zuwa New Delhi, babban birnin Indiya mai nisan kilomita kusan 500 daga yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.