Isa ga babban shafi

Mutum daya ya mutu, 36 sun jikkata sakamakon wata fashewa a India

Mutum daya ya mutu sannan 36 suka jikkata a yau Lahadi, sakamakon fashewar wani abu a lokacin da ake gudanar da ibada a coci da ta hada mutane sama da 2,000 a kudancin India.

Wani wurin ibada a kasar India
Wani wurin ibada a kasar India wikipedia
Talla

Yan Sanda sun gano wanda ke da hannu a wannan lamarin kuma sun dauki tsauraran matakai," in ji daraktan 'yan sandan jihar Kerala Darvesh Saheb ga manema labarai.

Masu ibada a cikin Coci
Masu ibada a cikin Coci © Véronique Gaymard/RFI

"Bincike na farko ya nuna cewa fashewar wani abu ne, Kerala Darvesh ya kara da cewa mutum daya ya mutu, wasu 36 kuma suna karbar magani.

Jami’in ya ce fashewar ta faru ne da misalin karfe 9:40 na safiyar  Lahadi a dakin taro na kasa da kasa na Zamra da ke Kalamassery, inda sama da mutane 2,000 suka hallara domin taron kwanaki uku na mabiya Jehobah.

Coci
Coci © FB

Kamfanin dillancin labarai na PTI (Press Trust of India) ya ba da rahoton "fashewa" guda uku a safiyar yau Lahadi a wannan gari da ke kusa da tashar jiragen ruwa na Kochi.

Indiya tana da al'uma kusan biliyan 1.4, fiye da kashi 2% daga cikinsu Kiristoci ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.