Isa ga babban shafi

Za a daina aikin agaji a Gaza saboda rashin man fetur

Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa dole ta dakatar da ayyukanta a karshen wannan rana ta Laraba a Gaza ganin yadda fetur da suke amfani da shi ke karewa. 

Wata motar Majalisar Dinkin Duniya a wani yanki na Gaza.
Wata motar Majalisar Dinkin Duniya a wani yanki na Gaza. AFP - MAHMUD HAMS
Talla

Hankula na ci gaba da tashi a game da yadda matsalar jinkai ke da ta’azzara a yankin Zirin Gaza da ke ci gaba da shan luguden wuta daga  Isra’ila, inda wani likita  ya bayyana yadda ya zame masa dole ya yi wa wani mutum wanda ya ji rauni aiki ba tare da ya ba shi allurar kashe zafi ba. 

Isra’ila ta yanke wa Zirin Gaza ruwa da wutar lantarki da sauran mahimman ababen more rayuwa, kuma manyan motocin dakon kaya 70 makare da kayayyakin agaji ne suka shiga wannan yankin tun da aka fara yakin, wanda magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ba za su wadatar ba. 

Isra’ila ta kaddamar da munanan hare-hare a kan Zirin Gaza a matsayin martini ga harin da mayakan Hamas suka kai cikin yankinta, inda suka kashe mutane dubu 1 da dari 4, suka kuma yi garkuwa da mutane 222 a ranar 7 ga watan Oktoba. 

Firaminista Benjamin Netanyahu  ya sha alwashin kawar da  kungiyar Hamas, kuma yanzu haka hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza sun yi sanadin mutuwar mutane dubu 5 da dari 8 a yankin, cikin su har da yara kanana da dama

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.