Ya kamata a samar da shiri na musamman domin kula da lafiyar kwakwalwa - WHO
Ranar 10 ga watan Oktoban kowacce shekara, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar tunatar da jama'a muhimmancin kula da lafiyar kwakwalwa, da kuma nuna goyon baya ga masu fama da matsalolin da suka danganci kwakwalwa.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:00
Matsalolin lafiyar kwakwalwa, wanda ya hada da cutar damuwa, firgita, amfani da kayan maye, cin zarafi, tashe-tashen hankula, rashin kula da lafiyar mata masu juna biyu da kuma yayin haihuwa, su ne manyan abubuwan da ke haifar da matsalolin da suka shafi lafiyar kwakwalwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, tanayin lafiyar kwakwalwa na da tasiri mai mahimmanci a kan ci gaban matasa fiye da biliyan daya da kuma zamantakewa da tattalin arziki, ciki har da samar da aikin yi a sassan duniya.
Duk da haka, WHO ta ce, yana da mahimmanci a samar da tsarin kula da lafiyar kwakwalwa a cibiyoyin kiwon lafiya, tare da hadin gwiwar kungiyoyin kasa da kasa.
Hukumomin lafiya na duniya sun yi imanin cewa, babban abin da ke haifar da matsalar kwakwalwa shine yadda ake nuna wariya ga wasu mutane, da kuma yadda rikice-rikice ke kara jefa al’ummar duniya cikin mawuyacin hali.
Shiga alamar sauti, domin sauraron rahoton Bilyaminu Yusuf.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu