Isa ga babban shafi

Farashin man fetur ya tashi a Duniya sakamakon yakin Isra'ila da Hamas

Yau Litinin anga hauhawar farashin man fetur a kasuwannin duniya wanda ya karu da akalla kashi biyu cikin dari dai dai lokacin da yaki ke ci gaba da tsananta a yankin gabas ta tsakiya tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta yankin Falasdinu.

Masana sun alakanta hauhawar farashin na man fetur da yakin da ak faro tsakanin kungiyar Hamas da Isra'ila.
Masana sun alakanta hauhawar farashin na man fetur da yakin da ak faro tsakanin kungiyar Hamas da Isra'ila. AP - Themba Hadebe
Talla

Farashin danyen man ya karu da akalla kashi 2.28 zuwa 2.7 wanda ya mayar da farashin duk ganga guda kan dala 86.86 yayinda farashin man nau'in na Amurka ya karu zuwa dala 85.27 bayan hauhawarsa da kashi 2.44.

Hauhawar farashin na yau Litinin, ya warware koma bayan da bangaren man ya fuskanta a makon jiya, wanda ya zama karon farko da aka ga faduwar farashin danyen man tun daga watan Maris lokacin da ya fadi da kashi 11.

Karuwar farashin dai na da nasaba da bukatar man a kasuwannin duniya saboda fargabar abin da kaje ya zo game da yakin da ya faro tsakanin Hamas da Isra'ila.

Tamas Verga na kamfanin PVM ya bayyana cewa galibi a duk lokacin da aka samu hatsaniya ko barkewar yaki a gabas ta tsakiya kai tsaye hakan na shafar farashin man fetur.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.