Isa ga babban shafi

Wani magidanci zai yi yarin shekaru 2 a Amurka saboda taba cinyar wata Mata

Kotu a Amurka ta aike da wani mutum gidan yari na kusan shekaru 2 bayan samunsa da laifin zura hannu a cikin siket din wata fasinjar jirgi lokacin da suke tsaka da bulaguro daga Cleveland zuwa Los Angeles da nufin taba cinyarta ta na tsaka da barci.

Kotun ta Amurka ta zargi Mohammad Jawad Ansari da yunkurin keta haddin matar.
Kotun ta Amurka ta zargi Mohammad Jawad Ansari da yunkurin keta haddin matar. © REUTERS
Talla

Rahotanni sun ce mutumin wanda aka bayyana sunanshi da Mohammad Jawad Ansari mai shekaru 50, ya zura hannunsa cikin siket din matar wadda makwabciyarsa ce a kujerar jirgi, lokacin da ta ke tsaka da barci, lamarin da ya farkar da ita cikin gaggawa tare da kai kararsa ga jami’an jirgin.

A cewar bangaren masu gabatar da kara, lamarin ya faru ne cikin watan Fabarairun shekarar 2020, kuma kai tsaye an bayyana yunkurin na Ansari da keta haddin mata.

Ansari wanda ya jima ya na musanta wannan zargi, sashen shari’ar na Amurka ya ce babu hujjojin da ke tabbatar da bai aikata abin da ake tuhumarsa ba, yayinda matar ta gabatar da tarin hujjoji, lamarin da ya kai ga zartas masa da hukuncin bayan shafe kwanaki 4 a jere ana shari’ar.

Alkali Fernando Aenlle-Rocha da ya jagoranci shari’ar ta jiya Alhamis ya kuma ci tarar Ansari dala dubu 40 baya ga hukuncin na daurin watanni 21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.