Isa ga babban shafi

Ku daina hana mu daukan mataki akan barayin ma’adinai da sunan kare hakki - Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewar kasashen Afirka ba za su amince da yadda manyan kasashen duniya ke amfani da sunan kare ‘yancin Bil Adama wajen hana su daukar matakan da suka dace domin bunkasa bangaren tattalin arzikin su ba, ta fuskar hukunta masu kwashe ma’adinai suna ficewa daga nahiyar  su ta barauniyar hanya ba. 

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayin gabatar da jawabi a zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu yayin gabatar da jawabi a zauren babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78 a birnin New York. © Reuters
Talla

Tinubu ya kuma bayyana cewar fasa kwabrin makaman da wadannan manyan kasashe ke kerawa zuwa nahiyar Afirka na matukar illa wajen durkusar da tattalin arzikin kasashen da ke yankin da kuma hana zaman lafiya. 

Shugaban Najeriyar ya bayyana haka ne lokacin da yake ganawa da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres a birnin New York, inda yace kasashen Afirka na fuskantar matsalar barayin ma’adinai dake lalata filaye tare da gurbata muhalli, inda suke kwashe zinare da sauran ma’adinan da ke karkashin kasa zuwa kasashen da suka ci gaba, a dai dai lokacin da ake barin yankunan da ake hakar su cikin tashin hankali. 

Tinubu ya ce a daidai lokacin da ake kare hakkokin mutanen da ke wannan aika aika, ya kuma dace a kare na mutanen da ke wadannan yankuna, wajen kare lafiyarsu. 

Shugaban ya ce ba za su yarda da yadda duniya ke musu caa ba akan kare hakkin Bil Adama, lokacin da suka dauki matakin kare lafiyar jama’arsu, saboda haka yake bukatar hadin kai domin magance wannan matsalar. 

Tinubu ya bukaci sauya fasalin Majalisar Dinkin Duniya ta yadda zata daina zama dandalin mahawara, zuwa bigiren da za’a dinga tattauna manyan batutuwan da suka addabi duniya da kuma sama musu mafita. 

Shugaban yace ganin irin talaucin da ya addabi kasashen Afirka da kuma matsalar tsaro da ayyukan ta’addancin da ke faruwa, ya zama wajibi ga shugabanni su yi aiki tare, domin kuwa duk wanda ya kauda kan sa daga Najeriya, na yiwa kan sa iila ne kawai. 

Tinubu ya shaidawa Guterres cewar ya yi fafutukar kafa dimokiradiya, an kuma tsare shi saboda haka, yayin da yace yanzu da ya zama shugaban kasa zai taimaka wajen ganin dimokiradiyar ta samar da irin ci gaban da Najeriya da Afirka ke bukata cikin gaggawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.