Isa ga babban shafi
G77+CHINA

Taron G77 ya bukaci soke basukan kasashe matalauta

Gwamnatocin duniya sun shiga rudu. Majalisar Dinkin Duniya,  hukumomin Bretton Woods da kuma ta kasuwanci l'OMC sun rasa kimar da suke da ita a duniya, don haka bai kamata ba mu ci gaba da kasancewa a rarrabe », in ji shugaban kasar Beazil Lui Inaacio Lula Dasilva a lokacin da ya ke jawabi ga taron tattalin arziki na gungun G77 tare da China.

El presidente brasileño Luiz Inácio Lula Da Silva durante su discurso en La Habana.
El presidente brasileño Luiz Inácio Lula Da Silva durante su discurso en La Habana. AP - Ramon Espinosa
Talla

Ya kamata kasashen duniya su kara hada karfi da karfe waje guda, domin  samar da haske a kokarin da ake na samar da juyin juya hali ga sha’anin masana’antu a duniya,  a cewar shugaban kasar mafi karfin tattalin ariziki a latin Amruka.

A jiya Assabar ne aka kawo karshen  zaman taron gungun G77 da China a La Havane da ke  kasar Cuba, inda da dama daga cikin wadanda suka yi jawabi a taron, suka bayyana rasahin samun  dai daito a duniya, da matsalar annobar Covid19 ta kara fitarwa fili, da kuma bukatar ganin an ragewa kasashe matalauta  basukan da ake binsu, domin samun damar amfani da kudin wajen yaki da dumamar yanayin a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.