Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kashe dalibai da malamai kusan 7,000 cikin shekara daya-MDD

Majalisar dinkin duniya ta sha alwashin kawo karshen ayyukan ta’addanci a makarantu, yayin da ake gwagwarmayar tabbatar da cewa kowanne yaro ya sami ilimin da ya kamata karkashin shirin ci gaba mai dorewa.

Babu wani dalili da zai sa a bar ta'addanci ya shafi ilimi, inji Antonio Gutteress
Babu wani dalili da zai sa a bar ta'addanci ya shafi ilimi, inji Antonio Gutteress AP - Khalil Senosi
Talla

Wannan na zuwa ne a shirye-shiryen da ake yi na marabá da babban taron majalisar dinkin duniya da za’a fara a makon gobe.

Ta cikin jawabin da ya gabatar kafin taron, Antonio Guttress ya ce rahoton da suka tattara daga hukumomin da ke da alaka da ilimi ya nuna cewa ‘yan ta’adda sun hari makarantu sama da 3,000 a sassan duniya a bara kawai, wato karin kaso 17 cikin dari na adadin da aka samu a 2021, sai dalibai da malamai 6,700 da aka kasha ko kuma aka yi garkuwa da su.

Antonio yace ya zama dole kowa ya bayar da gudunmowar da ake bukata wajen tseratar da ilimi daga fuskantar barzana, tare da cire siyasa wajen tafiyar da shi.

Ta cikin bayanin nasa, sakatare Janar Gutteress ya kuma bukaci kasashe musamman masu fama da harkokin ta’addanci da su kara kaimi wajen tattara alkalaman hare-haren da ake kaiwa cibiyoyin ilimi, abinda zai bada damar daukar matakan sa duka dace.

Matasa fiye da miliyan 224 ne a duniya ke da kishirwar ilimi kuma harkokin ta’addanci na taka rawa wajen haramta musu zuwa makaranta don haka ya zama wajibi a dauki mataki a cewar Gutteress.

Sakatare janar din ya kuma karkare jawabin nasa da taken “Zamu iya” “Dole muyi” “Mu kare ilimi daga hare-hare”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.