Isa ga babban shafi

Amurkawa na bikin cika shekaru 22 da kai hare-haren 11 ga watan Satunba

Bayan kammala ziyarar kwana guda a Vietnam, domin karfafa alakar tattalin arziki da kuma diflomasiyyar da ke tsakaninsu, shugaban Amurka Joe Biden ya kama hanyar komawa gida domin halartar taron tunawa da alhinin munanan hare-haren ta’addancin ranar 11 ga watan Satumba da aka kai wa Amurka, wadanda suka yi sanadin mutuwar dubban mutane.

Amurkawa na bikin tunawa da ciki shekaru 22 da kai harin 11 ga watan Satunba.
Amurkawa na bikin tunawa da ciki shekaru 22 da kai harin 11 ga watan Satunba. REUTERS - ANDREW KELLY
Talla

A bana dai shugaba Biden zai halarci taron cika shekaru 22 da hare-haren na ranar 11 ga watan Satumban shekarar 2001 ne a sansanin sojan Amurka da ke Anchorage a jihar Alaska.

Bayanai sun ce an yanke shawarar Biden ya halarci wannan biki a Alaska ne domin nuna cewar tasirin hare-haren na 11 ga watan Satumba ya shafi dukkanin sassan kasar Amurka, komai kuwa nisan da suke da shi.

A halin yanzu dai dubun dubatar mutane a sassan Amurka sun taru a manyan filaye da dakunan taruka da dakunan karatu da makabartu da dai sauran wurare domin alhinin tunawa da cika shekaru 22 da harin ta'addanci mafi muni da aka kai a kasar Amurka.

Kusan mutane dubu 3 suka rasa rayukansu, bayan da wasu ‘yan ta’adda suka yi amfani da jiragen saman  da suka yi  fashinsu wajen afka wa dogayen gine-ginen ma’aikkatar tsaro ta Pentagon da kuma ginin cibiyar kasuwanci ta  duniya da ke birnin New York,, yayin da ragowar jirgi guda da aka  yi nufin afka wa wani muhimmin ginin gwamnati a Washington ya fadi a wani da babu kowa a Pensylvania.

Idan za a iya tunawa dai, a wacccan lokaci, hare-haren  ne suka zama sanadin sanya Amurka aiwatar da muhimman sauye-sauye ga manufofinta na kasashen ketare, baya ga na cikin gida. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.